Labarai
Hukumar NAFDAC ta kwace kwayoyi da jabun magunguna na Naira biliyan uku a Kano.
Hukumar kula da ingancin magunguna da abinci ta NAFDAC ta kwace jabun kayayyaki da abinci da yakai kimanin Naira biliyan 3 a Kano.
Shugaban hukumar ta NAFDAC mai kula da jahar Kano Muhammad Shaba ne ya bayyana hakan lokacin da yake tattaunawa da filin Barka da hantsi a ranar litinin din makon da muke ciki.
Muhammad Shaba yace tun zuwan sa Kano a shekarar 2018 yayi kokari wajen hada kai da hukumomin tsaro da ya hada da hukumar hana fasa kwauri ta Custom da NDLEA wajen ganin an magance matsalar ta amfani da miyagun kwayoyin da jabun kayyyaki.
Muhammad Shaba yace hukumar ta NAFDAC tana bibiyar yadda kamfanin hada ruwa na leda dake tafiyar da hada ruwan ba tare da jamaa sun cutu ba.
Yace kuma sun hana gudanar da sanaar kamfanin na ruwa kusa da kwatami.
Yace a yanzu akwai sharioi dake gaban babbar kotun tarayya da ta shafi harkokin sha da fataucin miyagun kwayoyi.