Kiwon Lafiya
Hukumar NEMA ta bukaci mutanen Kano da Jigawa su bar wuraren da ake tsammanin samun ambaliya
Hukumar agajin gaggawa ta kasa NEMA reshen Jihar Kano, ta bukaci al’ummar jihar Kano da na Jigawa, da ke wuraren da ake fuskantar barazanar ambaliyar ruwada su tashi, don kaucewa afkuwar ta.
Wannan na kunshe ne cikin sanarwar da Shugaban gudanarwar na hukumar a nan Kano, Malam Nura Abdullahi ya sanya wa hannun.
Sanarwar ta bukaci al’ummar a jihohin biyu, su guji gina gidaje a kan hanyar ruwa, sannan su riga zubar da shara inda gwamnati ta kebe don samun saukin kwashe wa tare da kiyaye ambaliyar ruwa.
Sanarwar ta kuma ce, al’ummar su rungumi dabi’ar yashemagudanar ruwa tare da daina zuba shara a ciki, don kaucewa mummunar ambaliyar ruwa kamar yadda ta faru a karamar hukumar Jibia na jihar Katsina.