Connect with us

Kiwon Lafiya

Hukumar NEMA ta bukaci mutanen Kano da Jigawa su bar wuraren da ake tsammanin samun ambaliya

Published

on

Hukumar agajin gaggawa ta kasa NEMA reshen Jihar Kano, ta bukaci al’ummar jihar Kano da na Jigawa, da ke wuraren da ake fuskantar barazanar ambaliyar ruwada su tashi, don kaucewa afkuwar ta.

Wannan na kunshe ne cikin sanarwar da Shugaban gudanarwar na hukumar a nan Kano, Malam Nura Abdullahi ya sanya wa hannun.

Sanarwar ta bukaci al’ummar a jihohin biyu, su guji gina gidaje a kan hanyar ruwa, sannan su riga zubar da shara inda gwamnati ta kebe don samun saukin kwashe wa tare da kiyaye ambaliyar ruwa.

Sanarwar ta kuma ce, al’ummar su rungumi dabi’ar yashemagudanar  ruwa tare da daina zuba shara a ciki, don kaucewa mummunar ambaliyar ruwa kamar yadda ta faru a karamar hukumar Jibia na jihar Katsina.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,734 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!