Kiwon Lafiya
Hukumar NEMA ta ce ta karbo yan Nijeriya 141 da wasu mata 11 mata dauke da juna biyu daga kasar Libya
Hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA ta ce ta karbi akalla mutane 141 ‘yan asalin kasar nan daga kasar Libya, ciki har da mata 11 masu dauke da juna biyu.
Jirgin da ya dauko su daga Libyan ya sauka da karfe 10:45 na daren jiya Talata a filin jirgin saman Murtala Muhammad dake Lagos, bisa tallafin hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Duniya IOM.
A cikinsu akwai mata 71 sai kananan yara mata uku da jarirai mata uku, sai maza 53 da kananan yara maza 6 sai jarirai maza 3.
Da ya ke tarbarsu a filin Jirgin babban jami’in shirye-shirye na hukumar ta NEMA Injiniya Segun Afolayan, ya shawarci mutanen da ka da su bari abinda ya faru da su mara dadi ya yi tasiri a rayuwarsu.
Sannan ya bukace su su kasance masu sanin darajarsu da kuma nuna juriya yayin jimamin abinda ya same su, tare da mara baya ga yunkurin gwamnantin tarayya na kyautata dokokin shige-da-fice.
Tun a bara ne dai hukumar kula d ‘yan gudun hijira ta Duniya IOM take ta fafutukar ganin an dawo da ‘yan Najeriya da suka makale a kasar Libya zuwa nan gida Najeriya.