Kiwon Lafiya
Hukumar NERC ta ce zat asake nazarta tsarin biyan kudin wata
Hukumar kula da harkokin Lantarki ta kasa NERC ta ce za ta sake nazartar tsarin yadda masu amfani da wutar ke biyan kudin wutar a fadin kasar nan.
Cikin wata sanarwa da babbar jami’ar sashen yada labaran hukumar Vivian Mbonu ta bayar a jiya Talata, ta bayyana cewa hukumar za ta ci gaba da amfani da tsarin gano adadin karfin wutar Lantarkin da al’umma ke bukata a tsawon wani lokaci, tare da sanin nawa ya kamata su biya.
Vivian Mbonu ta kara da cewa za su nazarci tsarin domin sanin irin ci gaban da aka samu, kafin tunkarar shirin shekarar 2019 zuwa 2023.
Hukumar ta ce za ta yi hakan ne don ganin ta kyautata al’amuran samar da wutar lantarki a kasar nan.
A cikin makon jiya ne dai aka jiyo shugaban hukumar ta NERC James Momoh na cewa hukumar za ta daina amfani da tsarin, wanda aka bijiro da shi a shekrar 2008.