Kiwon Lafiya
Hukumar NHIA ta kaddamar da sabon shirin gaggawa don rage mutuwar jarirai

Hukumar Inshorar Lafiya ta Najeriya NHIA, ta kaddamar da wani sabon shiri na gaggawa domin rage mace-macen jarirai da ƙara samun damar kula da lafiyar jarirai a asibitocin gwamnati a faɗin ƙasar nan.
An kaddamar da wannan shirin ne a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano da ke jihar Kano, inda shugaban NHIA, Dr Kelechi Ohiri, ta ce shirin zai mayar da hankali kan jarirai da ke fuskantar matsalolin gaggawa bayan haihuwa.
Dakta Ohiri, wadda Dakta Salawudeen Sikiru ya wakilta, ta bayyana cewa shirin ya samo asali daga wani tsari na kulawa da lafiyar iyaye mata da aka fara fiye da shekara guda da ta gabata.
Jami’in ya ce yanzu haka NHIA tana ɗaukar nauyin kuɗin magani ga jarirai a asibitocin gwamnati, inda asibitoci ke karɓar kudaden da suka kashe a kowane mako bayan an tabbatar da bayanan jinya.
Dakta Salawudeen Sikiru,, ya ƙara da cewa shirin ba zai tsaya kawai kan kulawar gaggawa ba, domin bayan an ceto jaririn za a yi masa rajista a kan inshorar lafiya ta ƙasa don ci gaba da samun kulawa.
Shirin zai shafi iyalai marasa galihu ne kawai, tare da buƙatar lambar shaidar zama dan kasa ta NIN domin tabbatar da sahihancin rajista.
You must be logged in to post a comment Login