Labarai
Hukumar NiHSA ta yi gargadin samun ambaliya a wasu jihohin Najeriya

Hukumar kula da harkokin ruwa ta ƙasa, NiHSA, ta sanya jihohin Bayelsa, Kogi, Anambra, Delta da wasu jihohi a cikin matakin gargadin gaggawa saboda yiwuwar ambaliyar ruwa a makonni masu zuwa.
A cewar hukumar, rahotonnin yanayi da aka tattara sun nuna cewa yawan ruwan sama da kuma ƙarin ruwa daga manyan koguna na iya haifar da ambaliya a yankunan da ke kusa da kogin Neja da Benue.
Hukumar ta kuma yi kira ga hukumomin agaji, gwamnoni, da mazauna yankunan da su ɗauki matakan kariya tun kafin lamarin ya kai ga asarar rayuka da dukiya.
You must be logged in to post a comment Login