Labarai
Hukumar NRC ta ja kunnen jami’anta da ke Sifuri tsakanin Kaduna zuwa Abuja

Hukumar kula da sifurin jiragen kasa ta Njeriya NRC, ta buƙaci ma’aikatanta da ke aiki a layin jirgin kasa na Abuja zuwa Kaduna da su bi doka da ƙa’idojin aiki cikin tsanaki, musamman bayan hadarin da ya faru da jirgin a ranar 26 ga Agustan bana.
Babban Daraktan hukumar Dakta Kayode Opeifa, ne ya bayyana haka ne a Lagos yayin da ya ke gabatar da sakamakon binciken da aka gudanar kan hatsarin.
Ya ce kafin a dawo da jigilar fasinjoji, dukkan ma’aikatan za samu horo na musamman na kwanaki hudu daga ranar Litinin, 22 ga Satumba, domin tabbatar da tsaro da ingancin aikinsu.
A cewarsa ba za a fara jigilar fasinjoji ba har sai an tabbatar da komai ya koma daidai.
You must be logged in to post a comment Login