Labarai
Hukumar NYSC za ta fara sanya shekarun haihuwa a takardar shaidar kammala hidimar kasa
Hukumar kula da ‘yan hidimar kasa NYSC ta ce zata fara sanya shekarun haihuwa a jikin takardar shaidar kammala hidimar kasa, a wani bangare na magance matsalar amfani da shekarun bogi.
Hukumar tace yanke shawarar hakan na zuwa ne biyo bayan tattaunawa da hukumar shirya jarabawar kammala makarantun sakandire ta yammacin Afirka WAEC.
Shugaban hukumar NYSC na kasa Shu’aibu Ibrahim ne ya bayyana hakan, lokacin da yake gabatar da jawabi a wani taron karawa juna sani da aka shiryawa jami’an hukumar, wanda ya gudana a birbnin tarayya Abuja.
A cewar sa da dama daga cikin manyan makarantun kasar nan basa jin dadin yadda suke gabatar da shekarun haihuwar da dama daga cikin daliban da suka kammala karatu ga hukumar, sakamakon zargin cewa na bogi ne.
Ya kuma ce sanya shekarun haihuwa cikin takardar shaidar kammala hudumar kasa zai dakile matsalar sanya sunayen daliban da ake aikewa hukumar, kuma tun farko sunayen su basa cikin wadanda aka yi bikin daukar sabbin dalibai da su.