Connect with us

Labarai

Hukumar SEMA ta tabbatar da mutuwar mutane 6 a jihar Katsina sakamakon mamakon ruwan sama da iska

Published

on

Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Katsina SEMA ta tabbatar da mutuwar mutane shida a jihar, sakamakon wani mamakon ruwan sama da iska mai karfi da aka tafka a daren alhamis din da ta gabata.

Shugaban hukumar ta SEMA Alhaji Aminu Garba Waziri ne ya tabbatar da hakan, lokacin da yake zantawa da manema labarai yau juma’a a Katsina.

Aminu Garba Waziri ya ce mamakon ruwan saman da aka tafka a daren jiya yayi sanadiyyar lalata gidaje sama da dari biyar.

Alhaji Waziri yace mutane hudu ne suka mutu a yankin Kukar Gesa yayinda mutane biyu kuma suka mutu a yankunan Shinkafi da kuma Modoji.

Shugaban hukumar na SEMA ya kuma ce mutum biyar ne suka samu raunuka a yankin Kukar Gesa, tare da lalata gidaje lamarin da ya haifarwa mutane da dama rasa matsugunan su.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!