Labarai
Hukumar tace fina-finai ta kama na’urorin da ake buga hotunan batsa

Hukumar tace fina-finai da dab’i ta jihar Kano karkashin jagorancin Alhaji Abba El-mustapha ta gano tare da kama wasu na’urori da ake yin amfani da su wajen buga hotunan batsa ga masu sana’ar maganin Gargajiya a cikin wasu unguwannin Kano.
hukumar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa jami’in yada labaranta Abdullahi Sani Sulaiman ya fitar a daren ranar Lahadi.
Kayan da hukumar ta kama sun hada da komfuyutoci da kuma injinan buga hotuna wato Printer.
Da ya ke yin holin kayan da Hukumar ta kama, Darakan dab’i na hukumar Alhaji Abubakar Zakari Garun Babba, ya bayyana wuraren da aka kama kayan wadanda suka hada wasu unguwani a karamar Hukumar birnin da Kuma wasu kauyuka na karamar Hukumar Wudil.
Haka kuma ya bayyana takaicinsa kan yadda wasu ke fakewa da sana’ar buga takardu watau photocopy suke buga hotunan batsa, inda ya kara da cewa ko kusa ko alama Hukumar ba za ta lamunci hakan ta ci gaba da faruwa a fadin jahar Kano ba.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa har zuwa lokacin fitar da rahoton hukumar na ci gaba da rike kayan inda ta ke dakon shawarar lauyoyinta domin daukar mataki na gaba.
You must be logged in to post a comment Login