ilimi
Hukumar WAEC Ta Fitar Da Sakamakon Jarabawar 2023
Hukumar shirya jarrabawar Afrika ta yamma WAEC, ta fitar da sakamakon jarabawar kammala makarantun sakandare ta yammacin Afrika ta 2023 (WASSCE).
Shugaban hukumar Patrick Areghan, shugaban ofishin Najeriya (HNO) na WAEC, a yammacin Litinin din nan ya ce daga cikin mutane 1,613,733 da suka zana jarabawar, an hana sakamakon Ɗalibai 262,803 “saboda rahotannin da aka samu na magudin jarabawar.
Ya ce an samu ci gaba a fannin samun gurbin karatu a matsayin jimillan mutane 1,361,608, masu wakiltar kashi 84.38 cikin 100, sun samu kiredit da sama da haka a mafi karancin darussa biyar masu dauke da harshen Ingilishi ko lissafi.
Haka kuma, Ɗalibai 1,287,920, wadanda ke wakiltar kashi 79.81 cikin 100 na jimlarsu, sun samu kiredit da sama da haka a cikin mafi karancin darussa biyar, da suka hada da Ingilishi da Lissafi.
You must be logged in to post a comment Login