Connect with us

Labaran Kano

Hukumomin tsaro sun fara kai rangadi tashoshin zabe a Kano

Published

on

Gamayyar jami an tsaro karkashin kwamishinan ‘yansandan Kano Habu Ahmad sani sun fara zagayawa tashoshin zabe dangane da zabubbukan da za a sake gudanarwa a wasu kananan hukumomi 9 anan Kano.

Kwamishinan ya fara kai ziyara tashar zabe dake mazabar Kureken Sani a karamar hukumar Kumbotso.

Rundunar ‘yan sanda ta Kano ta ja hankali alumma kan zaben ranar Asabar

Rundunar ‘yan sanda ta samar da tsaro don tunkarar zaben da za’a a Kano

Kwamishinan ‘yansandan ya bayyana cewar gamayyar jami ‘an tsaron za su duk mai yuwa wajen an tababtar da an yi zaben cikin nasara ba tare wata matsala ba, kafin da ana zaben da kuma bayan zaben.

Wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya ruwaito cewar zaben na gudana lafiya a mazabar ta Kureken Sani

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 333,220 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!