Connect with us

Labarai

Yan sanda a Kano sun sanya dokar hana zirga-zirga a kananan hukumomi Biyu

Published

on

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta sanar da hana zirga-zirga a kananan hukumomin Dawakin Kudu da Warawa daga karfe 12 na rana zuwa 5 na yamma ranar Asabar, 20 ga Yuni, 2026, domin tabbatar da zaman lafiya yayin zaben cike gurbin kujerar Majalisar Wakilai.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Ibrahim Adamu Bakori, ya ce jami’an tsaro sun bazu a rumfunan zabe, cibiyoyin tattara sakamako da ofisoshin hukumar zabe domin kare lafiyar jama’a da tabbatar da sahihin zabe. Ya kara da cewa ma’aikatan INEC, masu sa ido kan zabe, ’yan jarida da jami’an da ke kan aiki ne kawai za su samu izinin zirga-zirga a lokacin.

Rundunar ta gargadi masu siyasa da magoya bayansu da su guji sayen kuri’u, tsoratar da masu kada kuri’a, satar akwatin zabe da yada labaran karya. Ta kuma bukaci al’umma su hada kai da jami’an tsaro tare da kai rahoton duk wani abu da zai iya tayar da zaune tsaye domin gudanar da zaben cikin lumana.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!