Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Hukuncin kisa ne ya fi dace wa ga masu fyade – Minista

Published

on

Ministan kula da harkokin mata Pauline Tallen ta bukaci da a rika aiwatar da hukuncin kisa kan wadanda aka kamasu da laifin fyade.

Pauline Tallen ta bayyana hakan ne lokacin da ta ke kaddamar da shirin amfani da iskar gas wajen girki da kuma dashen itatuwa a garin Girei da ke jihar Adamawa a jiya juma’a.

Ministar ta bukaci da a rika daukan tsauraran matakai akan mutanen da ke bautar da kananan yara da sauran wasu laifuka da dama.

Da ta ke jawabi kan muhimmancin amfani da Gas wajen girki kuwa, ministar ta ce, a kididdigar da hukumar lafiya ta duniya WHO ta fitar, ta ce, akalla mutane miliyan hudu da dubu dari uku ne ke rasa rayukansu a duk shekara sanadiyar cututtukan da suke dauka sakamakon rashin amfani da gas wajen girke-girke.

Saboda haka ta ce shugaban kasa ya amince a bai wa kowace karamar hukuma a kasar nan tukunyar gas guda dubu daya don rabawa jama’a.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!