Labarai
Hukuncin kotun ƙoli a shari’ar gwamnan Kano ya nuna bunƙasar dimukraɗiyya- Nasiru Garo
Kwamishinan ma’aikatar muhalli da sauyin yanayi a jihar Kano Nasiru Sule Garo ya bayyana hukuncin kotun ƙoli a matsayin tabbatuwar shugabanci na gari a Najeriya.
Haka kuma hukuncin ya nuna ƙarara yadda aka samu bunƙaaar dimukraɗiyya a Najeriya.
Nasiru Sule Garo ya bayyana hakan ta cikin saƙon taya murna ga gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir jim kaɗan bayan yanke hukuncin da kotun ƙoli ta yi a ranar Juma’a.
Kwamishinan ya kuma ƙara da cewa, ɓangaren shari’a ya tabbatar da cewa shi ne karfin marasa ƙarfi, sannan ya buƙace su da su ci gaba da zama abin koyi domin ci gaban tsarin dimokuraɗiyyar Nijeriya.
Garo, ya kuma buƙaci magoya bayan jam’iyyar NNPP na Kano da su dage da kuma ci gaba da baiwa gwamnati goyon baya don tabbatar da manufofinta.
You must be logged in to post a comment Login