Labarai
Human Right Watch ta bukaci majalisar dinkin duniya ta kare mata da yaran Sudan daga cin zarafi
Kungiyar kare hakkin Dan-adam ta Human Right Watch, ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya da ta kare mata da kannan yara daga cin zarafi ta hanyar lalata da su a Sudan.
Kungiyar, ta bayyana cewa aikata Fyaɗe da mayakan RSF ke aikatawa laifukan yaƙi ne.
Kungiyar ta Human Right Watch, ta ce, a tattauna da ya yi da wasu tarin mata da galibinsu aka yi musu fyade a gaban ƴan uwansu.
BBC, ta ruwaito cewa, a watan Oktoban da ya gabata ne wani binciken Majalisar Dinkin Duniya ya nuna cewa, matsalar aikata fyaɗe ta kai mataki mai ban tsoro kasar ta Sudan.
Haka kuma, Ƙungiyar ta yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ƙasashen tarayyar Afirka da su tura dakarun da za su bayar da tsaro tare da dakile irin wannan cin zarafin da kuma hukunta masu laifi.
You must be logged in to post a comment Login