Labarai
IBB ya sadaukar da gidan kakanninsa don gina Asibiti a Kano

Tsohon shugaban kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) ya bayyana kudirinsa na ci gaba da tallafawa ayyukan cigaba a fadin kasar nan. Ya bayyana haka ne yayin taron aza harsashin ginin asibiti da ya dauki nauyin ginawa a garin Kumurya, karamar hukumar Bunkure, Jihar Kano.
Janar Babangida wanda Janar Halliru Akilu ya wakilta, ya ce an gina asibitin ne a filin gidan kakanninsa, domin saukaka wa jama’ar yankin samun ingantacciyar kula ta lafiya.
A nasa jawabin, Mai Martaba Sarkin Rano, Alhaji Dr. Muhammad Isah Ummaru, wanda ya aza harsashin ginin, ya bayyana farin cikinsa da wannan gagarumin aiki da aka kawo a masarautarsa ta Rano.
Shi ma Dagacin Kumurya, Alhaji Salisu Musa Murabus, ya yi godiya a madadin al’ummar yankin, yayin da taron ya samu halartar Malam Ibrahim Khalil, Shugaban Majalisar Malamai ta Jihar Kano, da sauran manyan baki.
You must be logged in to post a comment Login