Labarai
ICPC ta hana Nasir El-Rufa’i zuwa asibiti domin a duba lafiyarsa – Muyiwa Adekeye

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ICPC ta hana tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, zuwa asibiti domin a duba lafiyarsa, a cewar mai magana da yawunsa, Muyiwa Adekeye.
Adekeye ya shaida wa DW Hausa cewa hukumar ta hana El-Rufa’i samun damar ganin likita duk da cewa yana fama da matsalar gani da ke buƙatar kulawar lafiya. Ya ce wannan mataki ya ƙara jefa damuwa kan yanayin lafiyar tsohon gwamnan.
Haka kuma, a watan Mayun da ya gabata, iyalan El-Rufa’i sun zargi hukumar ICPC da hana su kai masa abinci tare da takaita musu damar ganinsa. Sai dai babu wata sanarwa daga hukumar da ke tabbatarwa ko musanta waɗannan zarge-zargen.
You must be logged in to post a comment Login