Labarai
Yau shekaru 12 kenan cif da rasuwar Sarkin Kano na 13 marigayi Ado Bayero

Yau shekaru 12 kenan cif da rasuwar Sarkin Kano na 13 a jerin sarakunan Fulani, marigayi Ado Bayero, wanda ya rasu a ranar 6 ga watan Yunin shekarar 2014 bayan shafe sama da rabin ƙarni yana jagorantar masarautar Kano.
A cikin shekaru 12 da suka gabata tun bayan rasuwarsa, al’ummar Kano, Arewacin Najeriya da ma ƙasa baki ɗaya na ci gaba da tunawa da shi saboda irin gudunmawar da ya bayar wajen tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban al’umma. Marigayi Ado Bayero ya kasance ɗaya daga cikin sarakunan gargajiya da suka yi fice wajen kare martabar masarautar Kano tare da taka muhimmiyar rawa a harkokin zamantakewa da sulhu tsakanin al’umma.
An san shi da ƙoƙarinsa na ƙarfafa zaman lafiya tsakanin mabiya addinai da ƙabilu daban-daban, tare da bayar da gudunmawa wajen bunƙasa ilimi, kasuwanci da ci gaban jihar Kano. Haka kuma, salon shugabancinsa na tawali’u, haƙuri da kusanci da talakawa ya sa ya kasance abin ƙauna ga jama’a da dama.
You must be logged in to post a comment Login