Connect with us

Labarai

Hisbah a Kano za ta fara tantance wadanda suka nemi shiga shirin auren zawarawa

Published

on

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta sanar da cewa za ta fara tantance wadanda suka nemi shiga shirin auren zawarawa daga ranar Litinin, 8 ga Yunin 2026.

Arewa Updates ta rawaito cewa, sanarwar ta fito ne ta hannun Daraktan Wayar da Kai na Hukumar, Malam Auwalu Ado Sheshe.

A cewar sanarwar, Kwamitin Shirin Auren Zawarawa na Jihar Kano karkashin jagorancin Babban Kwamandan Hisbah, Sheikh Dakta Aminu Ibrahim Daurawa, ya bukaci duk masu neman cin gajiyar shirin da su gaggauta mayar da fom dinsu domin gudanar da gwajin lafiya da sauran matakan tantancewa.

Sanarwar ta bayyana cewa masu neman shiga shirin daga kananan hukumomi za su mika fom dinsu a ofisoshin Hisbah na yankunansu.

Haka kuma, daidaikun mutane da kungiyoyi za su kai fom dinsu zuwa Hukumar Yaƙi da Cutar Kanjamau ta Jihar Kano da ke Na’ibawa, inda za a fara tantance su daga karfe 8:00 na safe ranar Litinin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!