ilimi
Idan ana son zaman lafiya a biya mu haƙƙinmu – ASUU
Ƙungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa ASUU ta ce, idan ana son zaman lafiya a biya ta haƙƙi mambobinta na wata 8.
Kalaman ASUU na zuwa ne a matsayin martani ga gwamnatin tarayya biyo bayan fara biyan mambobin sabuwar ƙungiyar malaman jami’o’i ta CONUA albashin wata 8.
Da yake yiwa Freedom Radio ƙarin bayani, shugaban ASUU shiyyar Kano, Farfesa Abdulkadir Muhammad ya ce, rashin biyan su albashinsu ba zai hana su ɗaukan mataki na gaba ba.
“Muna da matakai daban-daban da za mu ɗauka, ba iya yajin aiki ba, amma zaman lafiya shi ne a biya mu a haƙƙinmu”.
Ya ci gaba da cewa “Haƙƙin mu ne a biya mu albashin wata 8 na yajin aiki, in har ana son wanzuwar zaman lafiya, don haka duk matakin da muka ɗauka a nan gaba kar ayi mamaki”.
A baya-bayan nan ne rahotanni suka nuna cewa, gwamnatin tarayya ta fara biyan albashin wata 8 ga mambobin ƙungiyar CONUA na lokacin da suka yi yajin aiki.
Idan za a iya tunawa gwamnatin tarayya ta yiwa ƙungiyar CANUA rijista a lokacin da ƙungiyar ASUU ke tsaka da yajin aiki, wadda kuma ake sa ran za ta maye gurbinta.
You must be logged in to post a comment Login