Manyan Labarai
Idan ba’a farga ba Yan siyasa zasu yi amfani da Almajirai a matsayin ‘’Yandaba- Sarki Sunusi II
Mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sunusi II yace matsalar Almajirci ba abu ne da ya shafi addini kadai ba illa abu ne da ya shafi zamantakewar al’umma yau da kullum.
Malam Muhammadu Sunusi II ya bayyana hakan ne a Alhamis din makon da ya gabata a taron da kungiyar dalibai Musulmi ta kasa ta shirya karo na 108 da ya gudana a jihar Ogun.
Sarkin yace Almajirai wasu al’umma ne da iyayen su ke turawa neman ilimi na Alkur’ani mai girma daga bisani su bige da barace barace da yin ayyukan wahala akan tituna.
Sarkin yace miliyoyin Almajirai ne ke yawo a titunan arewacin Najeriya duk da kokarin da gwamnatocin jihohi ke yi na maganin matsalolin inda ya roki ‘’yan Najeriya musamman musulmi da su rika haifar ‘’yan ‘’yan da za su iya daukar nauyi.
Jaridar Kano Focus ta rawaito cewa Muhammadu Sunusi II yace mafi yawan yaran da ke yawo a arewacin Najeriya a shekaru 20 masu zuwa sun kawo karfi kuma su ‘’yan siyasa zasu dauka a matsayin yan bangar siyasa indai har ba’a kula da su ba.