Connect with us

Labarai

Iftila’i: An yi garkuwa da ƴan kasuwar Kwari sama da 20

Published

on

Masu garkuwa da mutane sun sace ƴan kasuwar Kano sama da 20.

Rahotonni sun ce, an sace rukunin ƴan kasuwar Kantin Kwari a kan hanyarsu ta zuwa birnin Aba na jihar Abia.

Jami’in yaɗa labaran kasuwar Alhaji Mansur Haruna Ɗandago ya tabbatarwa da Freedom Radio faruwar lamarin.

A cewar sa, lamarin sun samu rahoton kuma sun sanar da hukumomin tsaro da gwamnati.

Karin labari:

Tsaro: Bayan shekara biyu an cafke wanda suka yi garkuwa da bature a Kano

Matsalar tsaro: Masu garkuwa da mutane sun sace wasu tare da ƙona motar jami’an tsaro a Kano

Ɗandago ya kuma ce, tuni suka kafa kwamiti domin yin addu’o’i kan Allah ya kuɓutar da su.

Wasu rahotonni dai sun ce, ƴan bindigar sun nemi a biya su diyyar kuɗi sama da miliyan 20, sai dai Ɗandago ya musanta labarin.

Zamu ci gaba da bibiyar wannan labari a nan gaba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!