Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Iftila’i: Gobara ta yi ajalin mutane huɗu ƴan gida ɗaya a Kano

Published

on

Wata gobara da ta tashi a unguwar Kurna babban layi da yammacin Talata ta yi sanadiyyar rasa rayukan mutane huɗu ƴan gida ɗaya.

Wani maƙocin gidan da lamarin ya faru ya shaida wa Freedom Radio cewa, gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe huɗu na yamma, ta kuma shafe kusan awanni biyu tana ci.

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da faruwar lamarin ta bakin mai magana da yawunta Saminu Yusuf Abdullahi.

Ya ce, sun samu labarin faruwar lamarin ta hanyar kiran waya da misalin ƙarfe 5:10 na yamma, daga wani mai suna Tijjani Mai Kuɗi.

Daga nan ne kuma suka tura jami’an su na Kurna da Sabon Gari inda suka kai ɗauki gidan sannan suka kashe wutar.

Labarai masu alaka:

Iftila’i: Gobara ta tashi a kasuwar ƴan katako da ke Na’ibawa

Yadda mutane 3 suka rasa rayukan su sanadiyar tashin gobara a Kano

Saminu Abdullahi ya ce, gobarar ta ƙone ɗakuna biyu da ɗakin girki, ta kuma rutsa da mutane biyar wanda huɗu daga ciki sun rasu nan take.

Waɗanda suka rasun, sun haɗa da Mubarak Aliyu Ilyasu mai shekaru 22, sai Fa’iza Aliyu Ilyasu mai shekaru 17.

Sai kuma Khalipha Aliyu Ilyasu ɗan shekaru 18, da kuma Suraj Aliyu Ilyasu mai shekaru 15.

Wadda kuma aka ceto ita ce, Khadija Aliyu Ilyasu.

A cewar sa, tuni aka miƙa gawarwakin da wadda aka ceto zuwa asibitin ƙwararru na Murtala.

Sai dai mai magana da yawun hukumar ya ce, har kawo lokacin da muƙe haɗa wannan rahoyo ba su kammala bincike kan musabbabin gobarar ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!