ilimi
Ilimi: Jigawa ta ɗauki nauyin ɗalibai zuwa ƙaro karatu a Sudan
Gwamnan jihar Jigawa Muhammadu Badaru Abubakar ya dauki nauyin ɗalibai 210 zuwa Sudan don ƙaro karatu kan aikin likitanci.
Mataimakin gwamnan, Alhaji Umar Namadi ne ya bayyana haka lokacin da shugaban ƙungiyar Editocin Najeriya, Mustapha Isah da mambobin kwamitin suka kai masa ziyarar ban girma a Dutse.
Namadi ya ce manufar ɗaukar nauyin ɗaliban shi ne, cike giɓin da ke akwai a ɓangaren kiwon lafiya.
Ya ce, ana sa ran ɗaliban bayan kammala karatunsu za su yi aiki a yankunansu don taimakawa harkokin lafiya a jihar, musamman ma yankunan karkara.
You must be logged in to post a comment Login