Labarai
Ina da nagartar da zan tsaya takarar shugaban ƙasa a 2023 – Yahaya Bello
Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya ce, yana da duukanin nagartar da zai iya tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023.
Yahaya Bello ya sanar da hakan yayin da ake hira da shi ta cikin wani shiri a gidan talabijin na Arise ranar Litinin.
Ya ce, a shirye yake ya karɓi ragamar shugabancin ƙasar nan daga hannun shugaba Muhammadu Buhari la’akari da kyakyawan rahoton da yake da shi a jihar ta Kogi.
“In sha Allah za a rantsar da ni a shekarar 2023 a matsayin zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, wanda zan karɓa daga hannun Buhari a ranar 29 ga watan Mayun 2023”.
“Zan fitar da Najeriya daga cikin halin ƙuncin da ta ke ciki da zarar na ɗare bisa karagar mulkin shugabancin ƙasa, musamman ma ayyukan ta’addanci, kuma wannan amsa kiraye-kirayen al’umma ne na buƙatar na tsaya takarar shugaban ƙasa” a cewar Yahaya Bello.
You must be logged in to post a comment Login