Siyasa
Ina fargabar tabbatar da tsarin zangon mulki na 3 -Kabiru Dakata
Fitaccen dan gwagwarmayar nan Kwamaret Kabiru Sa’id Dakata ya bayyana fargabarsa kan yunkurin samar da tsarin baiwa shuwagabanni damar yin zango na uku akan karagar mulki.
Kwamaret Dakata ya bayyana hakan ne ta cikin shirin Kowane Gauta na Freedom Radio inda yayi tsokaci kan sabon kudirin baiwa shuwagabanni zango na 3 da wani dan majalisa na jam’iyyar APC ya shigar a cikin kunshin majalisar kasar nan.
Dan gwagwarmayar ya kara da cewa wannan kudiri ya zama tamkar wata fitilar da zata haskakawa ‘yan kasa ra’ayin wasu akan shugaba Buhari na dawowa karagar mulki a zagaye na uku.
Sannan za’a iya amfani da wannan kudiri a matsayin hanyar jarraba kwakwalan ‘yan kasa domin jin ra’ayinsu akan hakan, wanda zai iya bada dama wajen tan-tance ma’abota goyan baya da kuma wadanda basu da ra’ayin hakan a cewar Kwamaret Dakata.
Kazalika Kwamaret Dakata ya ce akwai bukatar a fayyace wannan kudiri a fili domin ‘yan kasa su fahimci gaskiyar abinda ke ciki.
Labarai masu alaka:
Zargin Tazarcen Buhari: Mai yasa Osinbajo yake shan mazga?
Wani matashi ya yanka rago da canza sunan sa zuwa Muhammad Buhari