Labaran Kano
Ina matukar kaunar harshen Hausa – farfesa Nina Pawlak
Farfesa Nina Pawlak ta bayyana yadda take matukar kaunar harshen Hausa lamarin da ya sanya har ta karanci harshen na Hausa a matsayinta na ‘yar Baturiya.
Farfesa Nina malamace a jami’ar Warsaw dake kasar Poland a sashin nazarin kimiyyar Harsuna, ta karanci harshen Hausa kuma har ta zama Farfesa a bangarang.
Haka kuma farfesa Nina ta bada gudunmawa sosai wajan yadawa da kuma koyar da harshen Hausa a kasar ta Poland sannan kuma ta duba ayyukan kammala digiri na uku ga wasu daga cikin manyan malamai a jami’ar Bayero dake nan Kano.
Farfesa Hafizu Miko Yakasai dake sashin nazari da bincike kan kimiyyar furuci da harsuna a jami’ar Bayero ya bayyana irin yadda farfesa Nina Baturiya ‘yar kasar Poland ta yiwa harshen Hausa aiki wajan koyo da koyar dashi a nahiyar Turai sama da shekaru hamsin 50.
rundunar yansandan kano ta musanta cewa jami’anta sun yi harbi mutane a Ado Bayero Mall
An bude sabbin filayen noman rani a jami’ar Bayero
Hukumar shige da fice ta ja kunnen wasu jami’anta kan cin hanci
Farfesa Miko ya kara da cewa jami’ar ta Bayero ta ka gyayato farfesa Nina domin a karramata a gaban masana daga jami’o’i daban-daban duba da irin tagomashin da harshen Hausa ya samu daga gareta.
Farfesa Nina Pawlak tace babban burinta a yanzu haka shine taga ta fassara kamus din Hausa zuwa Harshen Hausa a kasar su don mutanansu su amfana dashi a wannan zamani.