Labaran Kano
Ina rokon Ganduje ya rushe shirinsa na rarraba masarauta -Sheikh Dahiru Bauchi
Danna hoton dake sama domin sauraron cikakken jawabin Sheikh Dahiru Usman Bauchi.
Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan kuma jigo a darikar Tijjaniyya Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya roki gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje kan ya dakatar da shirinsa na rarraba masarautun jihar Kano bayan da kotu ta rushe su.
Cikin wani fai-fan sauti da aka nada, Sheikh Dahiru Bauchi ya bayyana cewa “na samu labarin da bashi dadi cewa har yanzu gwamnan Kano Ganduje yana neman ya dawo da masarautu wadanda kotu ta rushe wato
Ya ce yana so wakilai su sake bashi dama ya nada sarautunnan da kotu ta rushe kamar yana son rarraba kawo nan ‘yan Kano ne da Najeriya kuma hakan zai kawo rashin zaman lafiya,’ ”
Ina rokon Ganduje ya nema mana zaman lafiya a Najeriya ba iya Kano kadai ba,”
Sheikh Dahiru Bauchi ya kara da cewa “domin dukkanmu ‘yan Tijjaniyan Najeriya muna tare da maimartaba Sarkin Kano muna tare da fadar Kano, abinda duk ya taba sarkinnan ya tabamu gaba daya kuma ba zamu kyale ba.
Ina jawo hankalinsa ya janye maganar nan, yadda kotu ta rushe wadannan abubuwa nasa to ya hakura, tunda an maida Kano kamar yadda take, kamar shekara dubu da wani abu…”
Idan zaku iya tunawa dai a watan Mayun da ya gabata ne, gwamnatin jihar Kano ta kirkiri sabbin masarautu guda hudu a jihar wadanda suka hadar da Gaya, Rano, Karaye da kuma Bichi.
Sai dai,a watan Nuwamban da ya gabata ne babbar kotun jihar Kano, ta rushe kir-kirar masarautun.
Labarai masu alaka:
Kai-tsaye : Alkali Usman Na’abba ya yi hukuncin rushe kirkirar karin masarautu 4
Gwamnatin Kano ta amince da dokar dawo da masarautu hudu
An yi zangazangar kin amincewa da kara masarautu a Kano