Labarai
INEC na shirin fara rajistar masu kaɗa ƙuri’a a Dala

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, ta sanar da cewa za ta fara rajistar masu kaɗa ƙuri’a a dukkanin yankuna na Ƙaramar Hukumar Dala, daga ranar 2 ga watan Fabrairu.
Jami’in Zaɓe na Ƙaramar Hukumar Dala, Alhaji A. A. Maulud, ne ya bayyana hakan yayin wani taron masu ruwa da tsaki kan harkokin zaɓe da aka gudanar a yankin.
A cewar sanarwar, da jami’ar yada labaran ta karamar hukumar Dala ta fitar Hassana Aminu, ta ce rajistar za ta shafi dukkan mutanen da suka cancanta amma ba su da Katin Zaɓe na Dindindin.
Haka kuma, aikin zai bai wa waɗanda katin zaɓensu ya lalace, ko ke da kuskure a bayanansu, da kuma waɗanda ke son canja wurin rajistarsu zuwa wata rumfar zaɓe ko jiha da suka zaune, damar yin gyara.
You must be logged in to post a comment Login