Labarai
INEC ta amince da sabbin jam’iyyun siyasa 14 da za su shiga harkokin zaɓe

Hukumar zaɓen Najeriya INEC ta amince da sabbin jam’iyyun siyasa 14 a ƙasar, da za su shiga harkokin zaɓukan ƙasar.
Cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na X, ta ce ƙungiyoyi 171 ne suka gabatar mata da buƙatunsu na yi musu rajista domin zama jam’iyyu a ƙasar.
INEC ta ce bayan nazari tare da ɗora buƙatun ƙungiyoyin a ma’aunin sashe na 222 na kundin tsarin mulkin ƙasar da sashe na 79 (1,2 da 4) na dokar zaɓe ta 2022 kan ƙa’idar zama jam’iyya.
”Daga ƙarshe ƙungiyoyi 14 ne suka cika ƙa’idar hukumar zaɓen, yayin da sauran ƙungiyoyi 157 suka gaza cika ƙa’idar”, in ji hukumar ta INEC.
You must be logged in to post a comment Login