Labarai
INEC ta ci gaba da yi wa sabbin jam’iyyu rijista

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya INEC, ta sanar da ci gaba da aikin yin rajistar sabbin jam’iyyun siyasa.
Hukumar ta bayyana cewa daga cikin ƙungiyoyi 14 da suka nemi rajista, guda takwas sun cika dukkan takardun da ake buƙata kamar yadda doka ta tanada.
Kwamishinan hulɗa da jama’a na hukumar, Mista Sam Olumekun, new ƴa bayyana hakan ya na mai cewa, ƙungiyoyin sun kammala shigar da bayanansu cikin tsarin hukumar, yayin da mataki na gaba zai kasance tantancewa da tabbatar da sahihancin bayanan da suka gabatar.
Mista Sam ya kuma ce, INEC za ta ci gaba da aiwatar da aikin rajistar jam’iyyun cikin gaskiya da adalci da kuma bin ƙa’ida, domin tabbatar da cewa duk wata jam’iyya da za ta samu sahalewar rajista ta cancanci shiga harkokin siyasa a Najeriya.
You must be logged in to post a comment Login