Labarai
INEC: wasu ‘yan NYSC sunyi watsi da tayin aikin zaben da za’a gudanar a jihar Anambra
Wasu daga cikin masu yiwa kasa hidima da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta saki sunayen su, a matsayin wadanda zasu gudanar da aikin zaben cike gurbin dan majalisar Dattawa da za’a gudanar ranar 13 ga watan da muke ciki, a jihar Anambra, sunyi watsi da tayin daukar aikin da akayi musu.
Wasu daga cikin ‘yan hidimar kasar da suka nemi a sakaya sunan su, sun bayyana cewa basu da sha’awar yin aikin zaben, sakamakon cewa hukumar ta INEC ta gaza biyan su kudaden alawus na aikin zaben gwamnan da sukayi ranar 18 ga watan Disambar bara.
Haka zalika ‘yan hidimar kasar sun kuma koka kan yadda wasu daga cikin su da suka yi aikin zaben, kuma sun riga sun kammala aikin su na hidimar kasa da har yanzu suke bibiyar hukumar da ta biya su hakkokin su, amma ta gaza biyan su
Jami’in hukumar ta INEC a jihar ta Anambra Ebenezer Olawale ya shaidawa manema labarai cewa daga cikin ‘yan hidimar kasa dubu bakwai da dari shida da hukumar ta fitar da sunayen su, mutum dubu hudu ne suka kai rahoton su ofishin hukumar a matsayin wadanda zasuyi aikin zaben ranar 13 ga watan da muke ciki na Janairu.
Mista Olawale ya lura da cewa hukumar ta INEC zata ajiye gurbi domin bawa wadanda suke da sha’ar yin aikin daga cikin ‘yan hidimar kasar dama,a duk lokacin da suke bukata kafin nan zuwa ranar zabe, inda ya jaddada cewa ba dole bane ga kowannen dan hidimar kasar yayi aikin zaben ba.