Ƙetare
Isra’ila ta ci gaba da kai hare-hare Gaza duk da yarjejeniyar tsagaita wuta

Ma’aikatar lafiya ta Gaza ta ce, hare-hare ta sama da Isra’ila ke kai wa sun kashe mutum biyar a kudancin Zirin, tare da jikkata wasu da dama.
Waɗan da suka ga harin a sansanin ‘yan gudun hijira na al-Mawasi sun ce Isra’ilar ta kai harin ne kan wani tanti.
Haka zalika sun tabbatar da cewa ta sake biyo baya da wasu hare-haren a kusa da asibitin Kuwait, abin da ya dugunzuma iyalan da ke fake a wajen.
Hamas ta kira harin da dabbanci – na kan-mai-uwa-da-wabi, wanda kuma ya saɓa da yarjejeniyar dakatar da buɗe wuta da Amurka ta samar- da ta fara aiki makwanni bakwai da suka wuce.
Rundunar sojin Isra’ilar ta ce ta kai harin ne a matsayin martani bayan da aka farmaki dakarunta.
You must be logged in to post a comment Login