Connect with us

Ƙetare

Isra’ila ta sake kai sabbin hare-hare a Lebanon

Published

on

Sojojin Israel sun kai hari ta sama kan wani ginin gidaje da ke tsakiyar birnin Beirut a ƙasar Lebanon, a wani sabon hari da aka kai yayin da rikicin Gabas ta Tsakiya ke ci gaba da ƙamari. Rahotanni sun ce harin ya auku ne a unguwar Aisha Bakkar, wadda ke kusa da babbar cibiyar kasuwanci a birnin, inda aka ga wuta da hayaki suna tashi daga ginin bayan harin.

 

Rahotanni sun ce wannan shi ne karo na biyu da Isra’ila ke kai hari a tsakiyar Beirut tun bayan da rikici ya ƙara tsananta a yankin. Rikicin ya ƙara kamari ne bayan ƙungiyar Hezbollah ta kai hari kan Isra’ila a matsayin martani ga kisan jagoran addinin Iran Ayatollah Ali Khamenei a hare-haren haɗin gwiwar Amurka da Isra’ila.

A halin da ake ciki, hukumomin Lebanon sun ce sama da mutane 759,000 sun rasa matsugunansu sakamakon hare-haren da ake ci gaba da kai wa a sassan ƙasar, yayin da jami’an agajin gaggawa ke ci gaba da kwashe waɗanda suka jikkata.

 

Rahotanni sun kuma nuna cewa an kai wasu hare-hare a kudancin Lebanon da suka yi sanadin mutuwa da jikkatar wasu mutane.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!