Labaran Wasanni
Iwobi na fatan Super Eagles za su samu tikitin Kofin Duniya na 2026

Dan wasan tsakiya na Super Eagles da Fulham, Alex Iwobi, ya bayyana cewa ‘yan wasan Najeriya na cikin yanayin jira da fatan alheri kan yiwuwar samun damar halartar Kofin Duniya na 2026, kamar yadda PUNCH Sports Extra ta ruwaito. Iwobi ya ce rashin samun tikitin gasar yana da matuƙar raɗaɗi ga ‘yan wasa da masu sha’awar kwallon kafa a fadin kasar nan.
Da yake magana kan fifikon lashe AFCON 2025 ko samun tikitin Kofin Duniya, Iwobi mai shekaru 29 ya bayyana cewa lamarin yana da wahala sosai. Ya ce duk da cewa lashe AFCON babban tarihi ne ga dan wasa, akwai ‘yan wasa da dama a cikin Super Eagles da har yanzu ba su taba zuwa Kofin Duniya ba, wanda hakan ke sanya burinsu ya fi karkata zuwa samun damar halartar gasar duniya.
Iwobi ya kara da cewa ba zai so ya zama mai son kai ba ta hanyar fifita lashe AFCON, alhali wasu abokan wasansa ba za su samu damar cika burinsu na zuwa Kofin Duniya ba. Ya ce shi tuni ya taba zuwa gasar, amma yawancin ‘yan wasan tawagar na yanzu suna da burin zuwa Kofin Duniya karo na farko a rayuwarsu.
A halin yanzu dai, Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya (NFF) na jiran hukuncin FIFA bayan da ta shigar da ƙorafi kan wasan daf da karshe da Najeriya ta buga da Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo, inda ta zargi Congo da amfani da ‘yan wasa marasa cancanta. Babban Sakataren NFF, Dr. Sanusi Mohammed, ya ce suna da hujjoji masu ƙarfi da ke nuna cewa an yaudari FIFA, kuma suna da fatan hukuncin zai iya sauyawa domin bai wa Najeriya damar zuwa Kofin Duniya na 2026.
You must be logged in to post a comment Login