Labaran Wasanni
Jadawalin FIFA na shekara: Najeriya ta ci gaba da zama a matakin da take a Afrika
Najeriya na mataki na biyar a jerin jadawalin da hukumar FIFA ta duniya ta fitar a nahiyar Afrika, yayin da kasar Belgium ke mataki na daya a duniya.
Kasar ta Belgium ta ci gaba da kare kambun ta na Kasan cewa ta daya a duniya a fagen kwallon kafa, Inda a bana ma ta zama zakara a karo na hudu.
Kasar Brazil ce ke take mata baya a matsayi na biyu, sai masu rike da kambun kofin duniya France na uku, yayin da kasar England ke matsayin na hudu, Argentina da ta lashe gasar kofin kudan cin Amurka da kuma kasar Italiya da ta samu nasarar daukar kofin nahiyar turai na mataki na biyar da na shida.
Ragowar kasashen sun hadar da Sifaniya a matsayi na bakwai da Portugal a na takwas Denmark da Netherlands na a na tara da kuma na goma.
A yayin da a nahiyar Afrika kasar Senegal ce ke jagoran tar jadawalin inda ta kasance a matakin farko, sai kasar Morocco, yayin da zakarun gasar Arab cup Algeria ke a matakin na uku, sai Tunisia a na hudu.
Zakarun gasar cin kofin nahiyar Afrika har sau biyar kasar Masar da kuma Najeriya da ta lashe gasar sau uku na matsayin na biyar da na shida. Inda masu masaukin baki a gasar kofin ta Afrika a shekara mai zuwa Kamaru na mataki na bakwai.
Ghana da Mali da Ivory coast da kuma Burkina Faso na matsayin na 8 da 9 dana goma da kuma sha daya.
Ragowar kasashen sun kunshi, Jamhuriyyar Dimokaradiyyar Congo a na sha biyu, sai Afrika ta kudu a na sha uku, kasar Cave Verde na mataki na sha hudu sai ta karshe kasar Guinea a matsayi na sha biyar.
You must be logged in to post a comment Login