Labarai
Jagoran ‘yan adawa a kasar Chadi ya zargi jami’an tsaro da yiwa iyalansa kisan gilla
Daya daga cikin jagororin ‘yan adawa a kasar Chadi ya zargi jami’an tsaro da kisan gilla ga iyalansa a birnin Ndjamena.
Yaya Diallo wanda tsohon madugun ‘yan tawaye ne ya ce jami’an tsaron sun kai harin ne a gidansa da ke birnin N’Djamena babban birnin kasar.
A zantawa da manema labarai Yaya Diallo wanda ke neman takarar shugabancin kasar ya ce lamarin ya faru ne a jiya Lahadi 28 ga watan Fabrairun shekarar 2021.
Haka zalika ya kuma zargi dakarun da ke kula da fadar shugaban kasa karkashin jagorancin daya daga cikin ‘ya’yan shugaba Idriss Deby da laifin kisan gillar.
You must be logged in to post a comment Login