Labarai
Jakadan Najeriya a kasar Chadi ya buya sakamakon barazana ga rayuwarsa
Jakadan Najeriya a kasar Chadi Muhammad Dauda ya buya sakamakon barazana da rayuwarsa da ya ce ana yi tun bayan ba’asin da ya bayar gaban kwamitin Majalisar Wakilai, kan badakalar da ake zargin ta wakana a hukumar leken asiri ta kasa NIA.
Jaridar Premium Times ta wallafa a shafinta na Intanet cewa gwamnatin tarayya ce ta baiwa Jakadan rikon kwaryar kujerar babban daraktan NIA sakamakon dakatar da mai rike da mukamin Ayo Oke da aka yi, bisa zargin badakalr kudade, domin samun damar gudanar da bincike.
Muhammad Dauda ya rike mukamin ne daga watan Nuwamban bara zuwa watan Janairun bana, kafin maye gurbinsa da Ahmad Rufa’i Abubakar
Daga bisani aka sake maida shi kan kujrearsa ta Jakadancin kasar nan a Chadi, amma ya yi ikirarin cewa rayuwarsa tana fuskantar barazana.
A jawabin da ya gabatar yayin bada ba’asi gaban kwamitin bincike na Majalisar Wakilai, Ambasada Muhammad Dauda ya zargi shugaban kwamitin da shugaban kasa ya kafa domin bincikar badakalar hukumar ta NIA Babagana Kingibe da hannun cikin wata almundahanar kudi.