Labarai
JAMB ta umarci jami’o’i su gaggauta kammala daukar ɗaliban bana

Hukumar Shirya Jarabawar Shiga manyan makarantun gaba da sakandare ta kasa JAMB ta umarci jami’o’in gwamnati da su gaggauta kammala daukar ɗalibai na shekarar 2025 kafin ranar 31 ga Oktoban bana.
A jadawalin da hukumar ta fitar, tace jami’o’i masu zaman kansu suma wajibi ne su kammala daukar ɗalibai kafin 30 ga Nuwamban shekarar nan, yayin da aka ba dukkanin manyan makarantu na gaba da sakandare – na gwamnati ko na ƙasa masu zaman kansu – wa’adin zuwa ƙarshen shekara.
JAMB ta ce hakan yana cikin jadawalin da aka amince da shi a taron da aka gudanar na tsare-tsaren ilimi a shekarar nan bisa jagorancin ministan Ilimi.
You must be logged in to post a comment Login