Labarai
JAMB ta yi hasashen samun kuɗaɗen shiga har fiye da naira biliyan 23 a bana

Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu ta Najeriya, JAMB, ta yi hasashen samun kuɗaɗen shiga watau IGR har naira biliyan 23 da miliyan 800 a shekarar nan da muke ciki ta 2026.
Hukumar ta ce hasashen ya biyo bayan ƙaruwa da yawan masu rubuta jarabawar shiga jami’o’i ta UTME, tare da matakan da ake ɗauka na inganta tsarin tattara kuɗaɗe da gudanar da jarabawa cikin gaskiya da tsari.
Haka kuma, JAMB ta sanar da shirinta faɗaɗa cibiyoyin rubuta jarabawar UTME a faɗin Najeriya, inda ake sa ran ƙara yawan cibiyoyin daga adadin da ake da su yanzu zuwa 1,000.
Hukumar, a ta kara da cewa, hakan wani mataki ne na rage cunkoso da sauƙaƙa wa ɗalibai tafiye-tafiye masu nisa da kuma bai wa kowa damar rubuta jarabawar cikin yanayi mai kyau.
You must be logged in to post a comment Login