Labarai
JAMB zata duba yuwuwar fara bada guraban karatu a mayan makarantu
Hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantun gaba da sakandire JAMB, ta ce tana dubu yiwuwar fara bayar da gurbin karatu ga dalibai a wannan shekara.
Wannan na cikin wata sanarwar da hukumar ta fitar mai dauke da sa hannun mai magana da yawun hukumar Fabian Benjamin.
A cewar sanarwar, hukumar ta JAMB za ta gana da shugabannin Jami’o’in kasar nan a yau Litinin, da nufin dubu tsare-tsaren da hukumar da za ta fitar don fara bai wa daliban gurbin karatu a Jami’o’in fadin kasar nan.
Ta ce, za a gudanar da tattaunawar ne kan bayar da gurbin karatu da kuma dabarun dakile cutar corona, a tsakanin dalibai da suka rubuta jarabawar
A cewar hukumar, hukumar za ta kuma dubu yiwuwar bai wa duk daliban da suka rubuta jarabawar JAMB gurbin karatu a Jami’o’in kasar nan, da nufin karafa musu kwarin gwiwa ta fannin neman ilimi.
You must be logged in to post a comment Login