Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Jami’an Customs sun kama kwayar Tramadol ta fiye da Biliyan 1

Published

on

Hukumar yaki da fasakwauri ta Nijeriya Customs, ta cafke tarin kwayar nan ta Tramadol da kudinta ya haura sama da biliyan daya a filin jirgin saman Murtala Muhammad, da ke jihar Lagos.

Babban jami’in hukumar a jihar Lagos Muhammad Yusuf, ne ya bayyana hakan a Larabar makon nan yayin zantawarsa da manema labarai.

Muhammad Yusuf, ya ce, sun samu nasarar cafke kwayar ne a tsakanin watan Janairu zuwa Mayu wanda aka shigo da su daga kasashen da suka hada da Pakistan da India.

Haka kuma ya ce, sun kama tarin kwayoyin ne sakamakon rahotonnin  sirrin da suka samu daga kwararrun jami’an hukumar  a filin jirgin saman  kuma da zarar sun kammala bincike za su mika kwayar ga hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta NDLEA domin daukar mataki na gaba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!