Ƙetare
Jami’an Ghana sun duƙufa wajen gano musababbin hatsarin jirgin sama

Jami’ai a Ghana su na gudanar da bincike domin gano musababbin hatsarin wani jirgin soji mai saukar ungulu da ya yi sanadiyar mutuwar ministan tsaro da na muhalli da wasu mutum shida.
Shugaban Ghana John Mahama ya tabbatar wa iyalan mamatan da al’ummar ƙasar cewa rundunar soji ta ƙaddamar bincike na musamma kan musassabin hatsarin.
Jirgin ya ya yi hatsari ne kan hanyarsa daga Accra zuwa wani taron yaki da hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba a garin Obuasi na yankin Yammacin ƙasar.
You must be logged in to post a comment Login