Labarai
Jami’an Hisba sun cafke mata masu zaman kansu
Jami’an Hukumar Hisba ta jihar Kano sun sami nasarar cafke wasu mata da maza da ake zargin suna zaman kansu a unguwar na’ibawa da ke yankin karamar hukumar Tarauni a nan Kano.
A cewar hukumar ta samu bayanan sirri ne cewa, akwai tarin mata da ake zargin masu zaman kansu ne a yankin Na’ibawa ‘yan katako wadanda suka yi sansani a wurin suna cin karensu-babu-babbaka.
Haka kuma hukumar ta ce, a binciken da ta fadada ta kara gano wani sansani a unguwar ja’in layin makabarta da ake zargin shi ma na mata masu zaman kansu har ma hukumar ta yi awon gaba da wani matashi da ya sha barasa ya kuma shiga cikin gidan mata aure yana marisa.
Yayin da Freedom Radio take tattaunawa da matashin bayan ya dawo hayyacinsa ya bayyana cewa matar gidan ce ta kira shi domin ya bata naira 200 za ta sayi fulawa.
Da yake Karin haske kan lamarin, babban darakta a hukumar Dr Aliyu Musa Aliyu ya ce sun sami mata biyu ma masu aure da kuma mata marasa aure a gidan , kuma ya ce za su mika wadanda aka kama din gaban kotu, yayin da za su nemi kotun da ta basu izinin rufe gidajen.