Labarai
jami’an hukumar DSS sun kama tsohon Gwamnan Benue Gabriel Suswam
Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta cafke tsohon Gwamnan jihar Benue Gabriel Suswam, sakamakon wata matsalar tsaro da ta kunno kai.
Hukumar ta cafke tsohon Gwamnan ne bayan da Gwamnan jihar na yanzu Samuel Ortom ya shigar da korafi gaban hukumar ta DSS yana mai zargin tsohon Gwamnan do kokarin yiwa al’amuran tsaro karan tsaye a jihar.
Rahotanni sun bayyana cewa a shekarar bara ne hukumar ta DSS ta cafke tsohon Gwamnan jihar ta Benue, bayan da ta bankado wasu manyan makamai da ake zargin mallakin Gabriel Suswam din ne.
Wata Majiya mai karfi ta tabbatar da cafke tsohon Gwamnan da hukumar DSS din tayi biyo bayan shigar da korafi da Gwamnan jihar yayi gaban ta.
Wata sanarwa da hukumar DSS ta fitar mai dauke da sa hannun kakakin ta Tony Opuiyo ta ruwaito cewa an samu makaman ne a shekarar bara a yankin Aguiyi Ironsi da ke Maitama a birnin tarayya Abuja.