Labarai
Jami’an Indonesia da Thailand sun fara aikin zakulo mutanen da Ambaliya ta hallaka

Hukumomin Indonesia da Thailand sun fara aikin share tarkace domin lalubo ɗaruruwan mutanen da har yanzu ba a gani ba, bayan ambaliyar ruwa da zaftarewar ƙasa da ya kashe aƙalla mutum 480 a kudu maso gabashin Asiya. Ruwan sama mai ƙarfi ya mamaye yankunan Indonesia, Thailand da Malaysia a makon da mukai bankawana da shi, wanda ya bar dubban mutane a maƙale ba tare da mafaka ko kayan agaji ba.
Adadin waɗanda suka mutu a Indonesia ya ƙaru zuwa 316, yayin da 289 har yanzu ba a kai ga gano su ba, a cewar sabbin alƙaluman da hukumar jin ƙai ta ƙasar ta fitar.
A Thailand, bayanai sun tabbatar da cewa, aƙalla mutane 162 ne suka mutu, inda hukumomin da abin ya shafa ke ci gaba da aikin lalube.
You must be logged in to post a comment Login