Labarai
Jami’an Kwastam sun cafke makamai a tashar ruwan Ikko
Jami’an hukumar yaki da fasa kwauri ta Nijeriya Kwastam, sun samu nasarar cafke wasu makamai da harsasai a tashar ruwan Lagos da ake zargin an shigo da su ne ta ɓarauniyar hanya.
Wani babban jami’in hukumar ya bayyana cewa sauran kayan da da hukumar ta gano sun haɗa da kakin sojoji da kuma miyagun kwayoyi.
Haka kuma ya kara da cewa makaman sun haɗa da bindigogi masu sarrafa kansu da kuma samfurin harba ka ruga.
Hukumar ta ce ta samu nasarar kwato kayayyakin ne yayin da ake duba kayayyakin da aka shigo da su cikin ƙasar.
BBC ta ruwaito cewa, Sai dai babu wasu bayanai na cewa ko an kama wasu da ke da alaka da kayan.
You must be logged in to post a comment Login