Labarai
Jami’an tsaro dauke da makamai sun mamaye harabar majalisar dokokin jihar Kano
Jami’an tsaro dauke da makamai sun mamaye harabar majalisar dokokin jihar Kano.
Wasu shaidun gani da ido sun ce da misalin karfe biyu na dare ne jamia’n tsaro cikin kwamban motoci goma suka mamaye harabar majalisar.
Rahotanni sun ce hakan ba ya rasa nasaba da zargin da ake yiwa wasu daga cikin ‘ya’yan majalisar da ke neman tsige shugaban majalisar Yusuf Abdullahi Ata.
A nasa bangaren kakakin rundunar yan sandan jihar Kano SP Magaji Musa Majiya ya tabbatar da cewa an tura ‘yansanda a harabar majalisar ne domin tabbatar da tsaro.
zuwa yanzu dai rahotonni sun bayyana cewa, akalla ‘yan majalisa 21 daga cikin 40 suka sanya hannu domin tsige shugaban majalisar Yusuf Abdullahi Ata, kamar yadda rahotanni ke bayyanawa.
Yanzu haka dai babu kowa a cikin harabar majalisar, sai dai wata majiya ta sanar da mu cewa masu yunkurin tsige shugaban majalisiar suna gudanar da taron sirri a wani wuri na daban.